✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 146 sun mutu, 150 sun ji rauni a turereniya a Koriya

Mutum 146 sun rasu, wasu 150 sun samu raunuka a wani turereniyar da aka samu a wurin bikin a birnin Seoul na kasar Koriya ta…

Akalla mutum 146 ne suka rasu, wasu 150 kuma suka samu raunuka a wani turereniya da aka samu a wurin biki a birnin Seoul na kasar Koriya ta Kudu.

Mace-macen sun auku ne a lokacin da mutane suka yi turereniyar ana tsaka da bikin Holoween, wanda ya tara dimbin mutane a wani tsukakken layi a birnin.

Wasu daga cikin wadanda suka samu rauni suna cikin mawuyacin hali, kuma Shugaban Hukumar Kashe Gobara na yankin Yongsan, Mista Choi Seoung-Beom, ya bayyana cewa akwai yiwuwar adadin wadanda suka rasu zai karu daga 146.

A cewarsa, an tura ma’aikatan ceto sama da 400 da motoci 140 domin gudanar da aikin agaji da jinyar wadanda suka samu rauni bayan faruwar lamarin a ranar Asabar.

Rahotanni sun nuna turereniyar ta fara ne a lokacin da mahalarta taron suka yi ta kokarin kurdawa su yi gaba a tsukakken layin, bayan adadin mahalarta ya yi ta karuwa har ya kai Dubai.

Wannan turereniya ta auku ne kusa da otel din Hamilton, wanda ya shahara da yin casu a birnin na Seoul.

Karin farko ke nan da ake gudanar da bikin Haloween tun bayan bullar cutar COVID-19, wadda ta sa aka kafa dokar bayar da tazara da haramta gudanar da taruka.