✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 154 sun bace bayan kifewar jirgin ruwa a Kebbi

Jirgin ruwan mai dauke da fasinja 180 ya kife bayan awanni da fara tafiya

Akalla mutum 154 ne a ake zullumin ruwa ya ci su bayan hatsarin jirgin ruwan da ya auku a Jihar Kebbi.

Hukumomi sun ce kimanin mutum 180 a cikin jirginsa a lokacin da ya kife a Karamar Hukumar Ngaski ta Jihar Kebi da misalin karfe 10 na safiyar Laraba.

“Jirgin ruwan ya dauki fasinjoji 180 da babura 30 kirar Bajaj. Fasinojin na hanyarsu ce ta zuwa kasuwa a Malele da ke Karamar Hukumar Borgu ta Jihar Neja daga Kebbi, kuma hatsarin ya faru ne awanni kadan bayan tashinsu,” inji Manajan Hukumar Kula da Rafuka ta Najeriya (NIWA) a Yauri, Jihar Kebbi, Yusuf Birma.

Da yake danganta aukuwar lamarin ga raunin jirgin ruwan, jami’in ya tabbatar da mutuwar mutum hudu, sannan an ceto 20 a raye, a yayin da ake kokarin ceto ragowar 156 da ba a gani ba.

Ana fargabar mutuwar fasinjojin da ba a kai ga tsamo su da ransu ba da wuri, duba da yadda aka samu jinkirin aikin ceto saboda karancin kayan aiki.

Majiyoyi sun ce baya ga fasinjojin, jirgin ruwan ya kuma dauko bahunan kasar masu hakar zinariya da wasu kayan mutane da ke hanyarsu ta zuwa kasuwar kauye.

Majiyoyi sun ce hukumomi na gudanar da aikin ceton ne da tsoffin kayan aiki, a yayin da wasu masu iyo kuma ke amfani da dabarun gargajiya wajen nemo mutanen da ba a gani ba, da suka hada da mata da kananan yara.

“Muna ci gaba da aikin ceto kuma lamarin ya faru ne saboda lodin wuce kima —jirgin ruwan ba shi da karfin daukar fasinja 180.

“Har yanzu ana neman mutum 156 da ba a gani ba, kuma ana kyautata zaton nutsewa suka yi a cikin ruwa,” inji Birma.

 

Daga Sagir Kano Saleh da Romoke W. Ahmad (Minna) da Aliyu M. Hamagam (Birnin Kebbi) da Zahraddeen Yakubu (Kano).