✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 17 sun mutu a hatsarin mota a Abuja 

Ana ganin cewa gajiya da gudun wuce kima ne ya haddasa hatsarin.

Akalla fasinjoji 17 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya afku a kan hanyar Kwali zuwa Abaji da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Mukaddashin shugaban Hukumar Kiyawa Hadura ta Kasa (FRSC), Dauda Ali Biu wanda ya tabbatar da haka ya gargadi direbobi a kan karya ka’idojin tuki da gudun wuce kima.

Biu, ya yi wannan kiran ne yayin da yake bayyana cewar za a iya kaucewa afkuwar hatsarin wanda ya faru da misalin karfe 6 na safiyar ranar Talata.

Kakakin FRSC, Bisi Kazeem, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce wasu mutane hudu da ke cikin motar sun samu raunuka, yayin da aka ceto wani mutum daya a cikin motar ba tare da ya ji rauni ba.

Ya kuma gargadi mutane kan yin tafiyar dare, haka kuma ya bukaci direbobi da su rika yin hutu na tsawon mintuna 30 bayan kowace awa hudu don gujewa fadawa yanayi na gajiya ko kasala.

“Bincike ya nuna cewa hatsarin ya rutsa da wata Tirela mai lamba BAU 632 XA da wata mota kirar Toyota bas mai dauke da lambar GME 201 ZU.

“Babban abin da ya haddasa hatsarin kamar yadda rahoton ya nuna shi ne, gudun wuce gona da iri da kuma gajiya,” in ji shi.

Sanarwar ta kara da cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Abaji yayin da aka ajiye ragowar wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa na asibitin.