Mutum 18 sun mutu a wani sabon hari a Filato | Aminiya

Mutum 18 sun mutu a wani sabon hari a Filato

    Dickson S. Adama, Ado Abubakar Musa, Jos da Abubakar Muhammad Usman

Akalla mutum 18 ne aka kashe wasu da dama kuma suka ji rauni a wani sabon rikici da ya barke a kauyen Ancha na Gundumar Miamgo a Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.

Lamarin na zuwa ne bayan kwana 10 da aka kashe wasu mutane a kauyen Rafin Bauna a karamar hukumar.

Kakakin rundunar soji ta ‘Operation Safe Haven,’ Manjo Ishaku Takwa ne ya tabbatar da faruwar lamarin, amma bai bayyana adadin mutanen da suka ji rauni ba.

Sai dai mai magana da yawun kabilar Irigwe, Davidson Malison, ya zargi Fulani da hannu a harin, inda ya ce mutane shida sun ji rauni, yayin da gidaje da dama suka kone kurmus, sannan maharan sun yi awon gaba da kayan abincin mutanen yankin.

Da yake musanta zargin, Shugaban Kungiyar Fulani ta Gan Allah (GAFDAN), Garba Abdullahi Muhammed, ya ce babu gaskiya cewa Fulani na da hannu a kai harin.

Ya ce, “Ba mu da masaniyar kai harin kuma ba mu yi mamakin ambatar sunanmu ba, saboda duk lokacin da wani abu ya faru sai a ce mu ne, wanda kuma hakan ba adalci ba ne.

“Idan za a tuna a ranar 2 ga watan Janairu an kai wa mutanenmu hari sannan aka kashe wasu a Rafin Bauna. Mun kai rahoton faruwar abun ga jami’an tsaro don yin bincike,” inji shi.

Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya bayyana damuwarsa kan harin, kazalika, ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da kokarin ganin bayan bata-gari a jihar.

Ya umarci jami’an tsaro da su bankado wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su.

Lalong ya kuma umarci Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar, da ta ziyarci yankin tare da tantance irin barnar da aka yi wa mazauna kauyen don tallafa musu.

Gwamnan ya jinjina wa jami’an tsaro kan yadda suke ci gaba da yakar masu garkuwa da mutane da kuma tseratar da rayuwar wadanda aka sace.

Ya tabbatar da cewa duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane zai fuskanci hukuncin kisa.