✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 1,940 sun kamu da Coronavirus a Najeriya —NCDC

NCDC ta sanar da adadin wadanda suka kamu da cutar na ranar Alhamis.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC), ta ce an sake samun mutum 1,940 da suka kamu da cutar COVID-19 a ranar Alhamis.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na intanet a ranar Juma’a.

Daga cikin jihohin da aka samu wadanda suka kamu, Jihar Legas ce a kan gaba da mutum 845, sai Birnin Tarayya, Abuja da aka samu mutum 734, sannan Jihar Oyo na da 120.

Ribas na da 69, Delta na da 30, Kaduna na da 29, Edo 21, Filato 20, Anambra da Enugu kowannensu na da mutum 11.

Jihar Osun tana da 10, Ekiti mutum takwas, sai Jihar Kano mai dauke da mutum biyar.

Ragowar sun hada da Bayelsa da Ogun suna da mutum hudu kowanensu, ita kuwa Katsina tana da mutum uku, Bauchi da Jigawa na da mutum daya kowannensu.

Adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya tun bayan bullarta ya kai 233, 353, kazalika an sallami 212,040 daga cibiyoyin killace mutane.

Yawan wadanda suka rasu a sanadiyyar COVID-19 a Najeriya, ya kai 2,991.