✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 2 da awaki 218 sun mutu a hatsarin Zariya

Hatsari tsakanin tirelar dabbobi da motar garin sabulu

Wasu mutum biyu sun rasu tare da awaki 218 a wani mummunan hatsari da ya auku a kan babban hanyar Kaduan zuwa Zariya.

An yi hatsarin ne tsakanin tirelar dabbobin da wata babbar mota mai dauke da garin sabulu da misalin karfe 6 na safe a unguwar Dogarawa, Zariya.

“Mutum biyu da awaki 218 sun mutu a hatsarin, wasu dabbobi 63 kuma suka tsira.

“Jami’anmu da ’yan kwana-kwan sun je da safiyar suka kashe wutar,” inji Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Kaduna, Hafiz Mohammed.

Ya ce jami’an sun yi nasara kubutar da mutu daya a wutar da ta tashi, sauran biyu kuma sun makale ne a cikin motocin da suka yi hatsarin.

Ya kara da cewa an tuntubi hukumomin yankin don tabbatar da an binne mushen dabbobin, saboda kar miyagu su rika zuwa suna sayarwa a kasuwanni.