✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 20 sun mutu a hatsarin mota a Oyo da Neja

Galibin hadurran da aukuwa saboda rashin kiyaye dokokin amfani da hanya ne.

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), ta ce akalla mutum 20 sun mutu sakamakon hadurran da suka auku a hanyar Ibadan zuwa Legas hadi da garin Mokwa a Jihar Neja.

Hukumar ta ce mutum 10 sun mutu, shida sun jikkata daga cikin 18 da hatsari ya rutsa da su a Ibadan, yayin da 10 sun rasu a hatsarin da ya uku a garin Makwa, Jihar Neja.

Mukaddashin Shugaban hukumar na kasa, Mista Dauda Biu, shi ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ta bakin jami’in wayar da kan jama’a na hukumar, Mista Bisi Kazeem ranar Talata a Abuja.

Biu ya nuna damuwarsa kan yadda masu abubuwan hawa ba su kiyaye dokokin amfani da hanya da kuma gudun wuce hankali.

Ya gargadi masu wannan hali su daina ko kuma su fuskanci fushin hukumar.

Ya ce, galibin hadurran da suka aukun, hakan ta faru ne saboda rashin kiyaye dokokin hanya.