✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 200 sun mutu a wani sabon rikici a Sudan

An kona gidaje, an kai wa asibitoci hari tare da wawashe kayan mutane a kasuwanni

Akalla mutum 201 ne suka mutu yayin da 98 suka jikkata a wani rikici da ya barke a Yammacin Darfur na kasar Sudan.

Wani jami’in da ke aiki da gwamnan yankin ne ya sanar a ranar Litinin cewa an kona gidaje, an kai wa asibitoci hari tare da wawashe kayan mutane a kasuwanni.

Hukumar kula da ’yan gudun hijira ta kasar Norway (NRC) ta bayar da rahoton cewa, dubban mutane ne suka rasa muhallansu sakamakon tashin hankalin da ya barke.

Rikicin, wanda ya barke a Al Kuraynik ranar Juma’a ya fantsama zuwa Al Geneina, hedikwatar Darfur a ranar Litinin.

Har yanzu dai ba a san abin da ya hadda tashin hankalin ba.

A cewar wasu rahotanni, rikicin ya faru ne tsakanin makiyaya da manoma da ke fafatawa kan wurin kiwo da ruwa.

Wasu rahotannin kuma sun yi nuni da cewa wani hari da ’yan ta’addan Rapid Support Forces, wadanda a da ake kira Janjaweed ne suka kai.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na Musamman a Sudan, Volker Perthes, ya bukaci gudanar da bincike mai zaman kansa kan musabbabin tashin hankalin.

An sha samun barkewar tashin hankali a cikin ’yan watannin nan a Jihar Darfur da ke Yammacin Sudan da kuma jahohin da ke makwabtaka da ita da kuma Darfur ta Kudu.

Rikicin yana barazana ga girbin amfanin gona da ke gabatowa.

Kungiyoyin bada agaji sun yi imanin cewa sama da mutum miliyan 18 za su fuskanci matsalar karancin abinci a watan Satumba mai zuwa sakamakon yadda rikici ke ci gaba da kamari a kasar.