✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 2,109 sun kamu da COVID-19 a mako 1 a Koriya

Hukumomin Lafiya a kasar sun nuna damuwa kan sake dawowar cutar.

Koriya ta Kudu ta ba da rahoton harbuwar karin mutum 2,109 da sabon nau’in cutar COVID-19 a cikin makon jiya, wanda ya kawo jimlar masu ita a kasar zuwa 8,125.

Ma’aiaktar Lafiyar kasar ta sanar a ranar Talata cewa daga cikin sabbin wandada aka gano daga ranar 25 ga Yuli, mutum 240 baki ne daga kasashen waje, sauran mutum 1,869 kuma sun harbu ne a cikin gida.

  1. Rikicin Filato ya lakume rayuka 17 da gine-gine 85 —’Yan sanda
  2. ‘Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Alhakin Al’umma Ne’

Ta ce cabbin mutum 1,929 da suka harbu sun fito ne daga wurare daban-daban daga cikin kasar.

A cewar Hukumar Kula da Cututtuka ta Koriya (KDCA), ta bayyana cewa yawaitar mutanen da suka harbu da cutar a cikin kasar ya nuna yadda take dada tasiri.

A halin da ake ciki, kasar ta tabbatar da samun Karin mutum biyu da suka kamu da samfurin COVID-19 na Delta.

Koriya ta Kudu ta ba da rahoton samun karin mutum 1,202 da COVID-19 ta harba cikin awa 24, wanda ya kawo adadin masu cutar zuwa 202,203 a kasar.

Yawan wadanda ke kamuwa da cutar a mako na haura mutum 1,000.