✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 222 sun sake kamuwa da cutar Kwalara a Haiti

An samu karin mutum 22 da suka riga mu gidan gaskiya a dalilin annobar.

Mutane 222 sun sake kamuwa da annobar Kwalara da ta barke a baya-bayan nan a kasar Haiti kamar yadda wasu alkaluman hukumomin lafiyar kasar suka zayyana.

Hukumomin Lafiya a Haiti sun bayyana karuwar masu kamuwa da cutar ce a daidai lokacin da kasar ke fama da tarin rikice-rikice.

Rahoton da Ma’aikatar Lafiyar kasar ta fitar ya bayyana cewa, fursunoni 14 a gidan yarin birnin Port-au-Prince sun mutu, adadin da ya kara alkaluman mamatan ya zuwa yanzu a kasar da ke fama da matsaloli barkatai ciki har da na rashin tsaro.

Alkaluma sun nuna daga ranar 13 zuwa 17 ga wannan wata na Oktoba da muke ciki, an samu karin mutum 22 da suka riga mu gidan gaskiya a dalilin annobar.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nuna matukar damuwa kan halin da kasar ta fada a ciki, yana mai bayyana shi a matsayin mai daukar hankali.