✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 23 sun rasu, 33 sun ji rauni a hatsarin tirela a Neja

Mutum 55 da shanu ne a cikin motar wadda direbanta da yaron motar suka tsere bayan hatsarin

Mutum 23 suka rasu a wani hatsarin mota a kauyen Masha, kan titin Makera zuwa Mokwa da ke Karamar Hukumar Mashegu a Jihar Neja.

Wasu mutum 33 kuma sun samu raunuka daban-daban sakamakon harin motar.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta FRSC reshen Jihar, Joel Dagwa ya ce hatsarin na yammacin ranar Litinin ya ritsa ne da wata tirela ce, kirar DAF.

Ya ce bayan gudanar da bincike hukumar ta gano cewa gudun wuce kima ne ummulhaba’isin hatsarin, kuma direban motar da yaronsa sun tsere.

Jami’an FRSC na aikin ceto a wurin da motar ta fadi

Rahoton ya bayyana cewar motar ta taso ne daga Jihar Kebbi dauke da shanu zuwa Jihar Legas.

Har wa yau, motar na dauke da mutum 55 maza a lokacin da hatsarin ya ritsa da su.

Wasu daga cikin mutane da dabobbin da tirelar ta dauko

Ya ce dn dauke wadanda suka ji rauni zuwa Babban Asibitin Mokwa, inda a nan ne likitoci suka tabbatar ra rasuwar 23 daga cikinsu.