✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 23,000 sun tsere saboda rikici a Kongo —MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutum 2,500 ne suka isa Uganda daga DRC

Mutum 23,000 sun tsere bayan sake barkewar fada tsakanin sojojin gwamnati da ’yan tawaye a Arewa maso Gabashin kasar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC).

Ofishin Kula da Harkokin Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar ya fada a ranar Litinin cewa kimanin mutum 2,500 ne suka isa Uganda daga DRC tun bayan barkewar rikici a yankin a ranar Alhamis.

Rahotanni daga yankin sun ce, an yi ba-ta-kashi tsakanin sojojin gwamnati da’yan tawayen a yankin Rutshuru da ke kusa da iyakar Uganda da Rwanda.

A cewar ofishin, “Daga watan Maris zuwa yanzu, rikicin ya raba mutum 186,000 da muhallinsu, wanda ya sanya mutanen da abin ya shafa karuwa zuwa 396,000.”

’Yan tawayen na M23, gamayyar sojojin da suka sha kashi a hannun sojojin Kongo ne a 2013 ne da kuma tsofaffin sojojin kasar da suka balle a 2012, suka hadu suka kafa kungiyar ’yan tawaye.”

Yankin Rutshuru da ke Arewacin Kivu, wurin ne mai arzikin ma’adinai.

A cewar Amurka, kimanin kungiyoyin ’yan tawaye 130 ne ke fafutukar ganin sun kwace yankin mai tarin arzikin zinari da lu’ulu’u da sauransu.