✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 3 sun gurfana a gaban kotu kan laifin tayar da zaune tsaye

Wasu mutum uku da ake tuhuma da laifin tayar da zaune a cikin mazauna unguwarsu ta Igbo-Olomu, sun gurfana a gaban wata kotun Majistire da…

Wasu mutum uku da ake tuhuma da laifin tayar da zaune a cikin mazauna unguwarsu ta Igbo-Olomu, sun gurfana a gaban wata kotun Majistire da ke Ikorodu a Jihar Legas.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, mutum ukun da aka gurfanar a gaban kotun, ana tuhumarsu da laifukan da suka hada da kawo fitina ta hanyar karya yarjejeniya zaman lafiya da aka kulla da su.

’Yar sanda mai gabatar da kara, Insfeta Adegeshin Famuyiwa, ta shaida wa kotun cewa mutanen da ake tuhuma sun aikata laifin da ake zarginsu da shi a tsakanin watan Fabrairun 2020 zuwa Janairun 2021 a kan layin Babatunde Lawal da ke yankin Owutu na Karamar Hukumar Ikorodu a Jihar Legas.

Famuyiwa, ta ce wadanda ake zargin ba su da abun yi face tayar da fitina da kawo hargitsi ta hanyar kulle kofar bandakin da mutane ke amfani da shi da zarar sun shiga biyan bukatarsu.

Ta ce sun kuma katse bututun ruwan da ke kai wa mazauna unguwar ruwan fanfo, wanda ya hadar da wanda ya ke bawa wasu shaguna ruwa a unguwar.

Ta kuma ce, wanda ake tuhuma sun yi karyar cewa matar da ta kai korafi caji ofis kan abin da suke aikata wa ta mari daya daga cikinsu, wanda hakan ya yi sanadiyar haifar masa da rauni a kunne sannan sun rika kiranta ‘Ashawo’ wato karuwa a bainar jama’a.

Alkalin kotun Mista B. A. Sonuga, ya bayar da belin kowane daya daga cikin wandanda ake tuhuma a kan Naira dubu dari biyu tare da neman su kawo mutane biyu da za su tsaya musu, sannan ya kuma dage zaman sauraron karar zuwa ranar 1, ga watan Fabrairun 2021.