Mutum 3 sun mutu sakamakon mamakon ruwan sama a Katsina | Aminiya

Mutum 3 sun mutu sakamakon mamakon ruwan sama a Katsina

    Bashir Isah

Rahotanni daga Karamar Hukumar Kankara a Jihar Katsina sun ce akalla mutum uku sun mutu sannan wasu da dama sun jikkata, kana gidaje masu yawa sun salwanta sakamakon ruwan sama mai yawa da aka samu a yankin.

Jami’in Yada Labarai na Karamar Hukumar, Abdulkarim Sani, shi ne ya bayyana wa manema labarai haka a ranar Lahadi, inda ya ce an fara ruwan saman ne a ranar Asabar da dare zuwa safiyar Lahadi.

A cewar jam’in, ruwan saman ya shafi wurare da suka hada da garin Kankara da Nasarawa da kuma Matsiga, tare da yin ajalin mutum daya a Nasarawa, biyu Matsiga.

Daya daga cikin marigayan, ajalinsa ya cin masa ne bayan da wani ginin laka ya rufta masa, inji jami’in.

Tuni dai aka yi jana’izar marigayan a ranar Lahadin bisa tsarin addinin Musulunci, kamar yadda Sani ya shaida wa manema labarai.

Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Katsina (SEMA), Umar Mohammed, ya tabbatar da aukuwar ibtila’in.

Mohammed ya ce, hukumar za ta ziyarci wuraren da lamarin ya shafa domin tantance barnar da ta auku.