✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 3 sun rasu, 17 sun ji rauni a hatsarin mota a Legas

An tabbatar da mutuwar mutum uku a hatsarin motar da wasu mutum 17 suka tsallake rijiya da baya.

Akalla mutum uku ne suka mutu yayin da wasu 17 suka tsallake rijiya da baya da raunukan da suka ji  a wani hatsarin mota da ya auku a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.
Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na yammacin ranar Laraba, inda ya rutsa da wata mota mai lamba GGE 584Y.
Da take tabbatar da hatsarin Abeokuta a ranar Laraba, Kakakin Hukumar kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) Rashen Jihar Ogun, Fluorence Okpe, ta ce lamarin ya rutsa da mutum 20, wadanda daga cikinsu mutum uku suka mutu, ragowar mutum 17 kuma suka jikkata.

A cewarta, ana zargin fashewar taya ce ya haddasa hatsarin da ya sa direban motar ya kasa rike ta.

Fluorence wadanda suka ji raunin an mika su zuwa asibitin Victory da ke Ogere don ba su kulawa, mamatan kuma aka ajiye su a dakin ajiye gawarwaki.
Ta kuma ambato Kwamandan FRSC na jihar, Ahmed Umar, yana jan hankalin masu tuka ababen hawa da su rika tabbatar da lafiyar tayoyinsu kafin su yi tafiya da su.

Sannan ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin.