✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Mutum 4 ’yan gida daya sun rasu a hatsarin kwalekwale a Taraba

Bayanai daga garin Ibbi inda kwalekwale ya nitse ranar Talata sun nuna mutum daga cikin wadanda suka riga mu gidan gaskiya ’yan uwan juna ne.

Bayanai daga garin Ibbi inda kwalekwale ya nitse ranar Talata sun nuna mutum daga cikin wadanda suka riga mu gidan gaskiya ’yan uwan juna ne.

Dan uwan wadanda suka rasu mai suna Umar Ibbi ya shaida wa Aminiya cewa mutane bakwai daga gidan Sarkin Pawan Ibbi ne suka shiga kwalekwalen da ya nitse a kan hanyarsu ta zuwa Kano domin yin ta’aziyyar kakansu.

Ya ce uku daga cikin mutanen ’yan gida ne suka tsira da ransu amma sauran su hudu duk sun rasu.

Umar Ibbi ya shaida wa wakilin Aminiya cewa dukkan wadanda suka rasu na da mata da ’ya’ya kuma yanzu haka ana zaman makoki a gidan Sarkin Fawan Ibbi.

Wata majiya daga bakin kogin Binuwai a garin na Ibbi ta nuna cewa an kara samun gawar mutum daya wanda haka din yasa adadin gawarwakin da aka tsamo daga kogin inda kwalekwalen ya nitse suka zama hudu.

Majiyar ta shaidawa wakilin Aminiya cewa har yanzu ba a gano wasu fasunjoji 13 daga cikin wadanda kwalekwalen ya nitse da su ba kuma ana ci gaba da neman sauran gawarwakin a cikin kogin na Binuwai.