✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalibai 3,000 sun sa hannu kan bukatar ABU ta koma bakin aiki

Jami'ar ABU ta fitar da sanarwa cewa sai 2023 za ta ci gaba da harkokin karatu

Sama da dalibai 3,000 ne suka rattaba hannu kan korafin da aka wallafa a intanet na neman Jami’ar  Ahmadu Bello (ABU) ta koma bakin aiki.

Kwanan nan aka ji jami’ar ta fitar da kalandarta ta shekarar karatu wadda ta nuna sai ranar 3 ga Janairun 2023 za a ci gaba da harkokin karatu jami’ar.

Aminiya ta kalato cewa, wani dalibi mai suna Ahmed Manga ne ya jangoranci kaddamar da korafin da ya soki jinkirin da jami’ar ke yi wajen komawa bakin aiki bayan sahafe wata takwas suna yajin aiki alhali ga takwarorinta sun yi nisa da karatu.

Sashen korafin ya nuna cewa, sabuwar kalandar karatu ta 2021/2022 da aka fitar ta kashe wa dalibai karsashin son komawa makaranta da suke da shi.

Ya kara da cewa, yayin da sauran makarantu suka yi nisa da karatu har ma an soma shirye-shiryen jarrabawa, amma hukumar ABU ta zabi ci gaba da zaunar da dalibai a gida har zuwa Janairu, 2023.

Majiyarmu ta ce, jan kafa da ABU ke yi wajen komawa bakin aiki ba ya rasa nasaba da matsalar kudi da take fuskanta biyo bayan umarnin Kotun Kwadago na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tsuke asusun jami’ar don biyan Naira biliyan 2.5 ga ma’aikatanta 110 da aka sallama daga aiki a 1996.

Bayan wallafawa, ya zuwa karfe 4:56 na yammacin Laraba, korafin ya samu sa hannu mutum 3,030 daga cikin 5,000 da ake bukata.

Sai dai hukumar gudanarwar ABU ta ce ba ta da masaniya kan korafin da aka wallafa a kanta a intanet, ta ce majalisar koli ta jam’iar ce ta fitar da kalandar karatu ta 2021/2022 amma ba ita ba.

Shugaban Sashen Hulda da Jama’a na jami’ar, Auwalu Umar, ya ce majalisar koli ta makarantar kadai ke da hurumin fitar da kalandar karatu don haka matsalar ba daga hukumar ba ce.