✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 32 sun kamu da sabon nau’in Coronavirus na Delta

Lamarin ya sake jefa kasar cikin annobar a zagaye na uku.

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da gano mutum 32 dauke da sabon nau’in cutar Coronavirus na Delta, lamarin da ya sake jefa kasar cikin annobar a zagaye na uku.

Shugaban Hukumar NCDC mai Dakile Cututtuka masu Yaduwa na Kasar, Dokta Chikwe Ihekweazu ne ya sanar da hakan a tanar Litinin.

Da yake zantawa da Kwamitin Kar-ta-Kwana da Shugaban Kasa ya kafa kan yaki da annobar Coronavirus, Dokta Chikwe ya ce an gano mutanen dauke da sabon nau’in cutar na Delta a wasu jihohi biyar na kasar.

A cewarsa, kashi 80 cikin 100 na gwajin da aka yi a jihar Akwa Ibom, an gano masu dauke da sabon nau’in cutar.

Sauran jihohin da Dokta Chikwe ya wassafa sun hada da Legas, Kuros Riba, Oyo da kuma birnin tarayya Abuja.

Ya yi gargadin cewa galibi wadanda suka kamu da sabon nau’in cutar matafiya da suka dawo Najeriya bayan balaguron da suka yi zuwa ketare.

A nasa jawabin, Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban Kwamitin, Boss Mustapha, ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen bullo da tsauraran mataki domin kare ’yan kasa.

Ya kuma jaddada muhimmancin sanya takunkumin rufe fuska wanda a cewarsa dokar tilasta sanya shi a bainar jama’a na nan daram har sai abin da hali ya yi.

A bayan nan ne wasu alkaluma na hukumomin lafiya suka nuna cewa sabon nau’in cutar mafi hatsari ya bazu zuwa kasashe 85.

Kawo yanzu annobar Coronavirus ta halaka mutane kusan miliyan 4 a fadin duniya, tun bayan soma bulla daga birnin Wuhan na kasar China a watan Disambar shekarar 2019.