✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 4 sun mutu a zanga-zangar karancin kudi a Edo 

Zanga-zangar ta hana bankuna da masu sana’ar PoS fitowa aiki.

Akalla mutum hudu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon zanga-zangar da ta barke kan karancin takardun kudi a Jihar Edo.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an shiga rudani saboda karancin takardun kudi yayin da bankuna da masu sana’ar PoS suka ki fitowa saboda fargabar kawo musu hari.

Mazauna jihar sun mamaye tituna don nuna rashin amincewarsu da gazawar janye tsarin canjin kudi da CBN ya fito, wanda hakan ya sanya suka shiga farfasa na’urorin cirar kudi na ATM a bankuna.

Akasarin bankunan da lamarin ya shafa sun hada da aUBA, Unity, Polaris, Access, Zenith da kuma First Bank.

Su ma dai masu sana’ar POS sun ki budewa saboda gudun hari musamman a Benin, babban birnin jihar.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu da CBN ya bayar na daina amfani da tsofaffin takardun kudi.

Sai dai bayan kara da wasu gwamnatocin jihohi suka shigar gaban Kotun Koli, Shugaba Muhammadu Buhari ya tsawaita wa’adin ci gaba da amfani da tsohuwar takardar Naira 200 har zuwa 10 ga watan Afrilu.

Tun bayan fito da tsarin takaita cire kudi da CBN ya fito da shi jama’a suka shiga korafin halin da za su tsinci kan su a ciki.

Wannan dai ta sanya masu karamin karfi da masu kananan sana’o’i shiga tsaka mai wuya bayan fara aiwatar da sabon kudin.