Mutum 4 sun mutu sanadiyyar rushewar bene mai hawa 3 a Legas | Aminiya

Mutum 4 sun mutu sanadiyyar rushewar bene mai hawa 3 a Legas

Yadda ake ci gaba da aikin ceto a wajen
Yadda ake ci gaba da aikin ceto a wajen
    Sani Ibrahim Paki

Wata mata mai sana’ar sayar da burodi da danta da kuma karin wasu mutum biyu sun mutu bayan wani bene mai hawa uku ya rushe a unguwar Ebute-Metta da ke Jihar Legas ranar Lahadi.

Rahotanni sun ce an kuma samu nasarar ceto mutum 23 daga cikin baraguzan ginin.

Benen dai wanda ke kan titin Ibadan Street ya rushe ne wajen misalin karfe 9:30 na daren Lahadin, kuma ana zargin har yanzu akwai ragowar mutane a cikin shi.

Tuni dai jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas da na takwararta ta ba da Agajin Gaggawa (LASEMA) suka dukufa aikin ceto a wajen.

Wata majiya ta ce ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, an ceto akalla mutum tara.

A wani bidiyon iftila’in a kafafen sada zumunta, an ga dandazon mutane sun yi wa wajen kawanya.

A cewar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), yanzu haka an samu tono gawar mutum hudun, a daidai lokacin da ake ci gaba da aikin ceto.