✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 4 sun rasu a hadarin mota a Oyo

Akalla mutum hudu sun rasa rayukansu yayin da wani hadarin mota a kauyen Seconner da ke kan hanyar Oyo zuwa Ogbomoso ta Jihar Oyo ya…

Akalla mutum hudu sun rasa rayukansu yayin da wani hadarin mota a kauyen Seconner da ke kan hanyar Oyo zuwa Ogbomoso ta Jihar Oyo ya ritsa da su.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura (FRSC) reshen jihar, CC Winifred U. Chukwurah ta tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin a ranar Laraba a garin Ibadan.

“Da gaske ne hadarin ya faru, shi yasa ko da yaushe muke ajiye jami’anmu a kan hanyar don tabbatar da masu ababen hawa na rage gudun wuce kima.”

“Amma duk da haka ba su daina ba, amma za mu ci gaba da fadakar da su,” in ji Chukurah.

Ta ce hadarin ya faru ne tsakanin wata karamar mota da babbar mota kirar Tirela, sakamakon gudun wuce kima.

Winifred ta gargadi masu ababen hawa a kan kiyaye dokokin tuki musamman kaurace wa gudun da ya wuce kima.

Wadanda suka rasu an garzaya da su zuwa dakin ajiye gawarwaki, yayin da wadanda suka jikkata ke samun kulawa ta kwararrun kiwon lafiya a asibiti.

Wani mutum da hadarin ya faru kan idonsa, ya shaida wa wakilinmu cewa mai babbar motar ne ya yi kokarin shan gaban wata mota yayin da birkin motar ya shanye.