✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 5 sun bace bayan fashewar sinadarai a Jamus

Har yanzu dai babu cikakkun bayanai kan musabbabin fashewar.

Akalla mutum biyar ne suka bace, da dama kuma suka jikkata bayan wani fashewar sinadarai a unguwar masana’antu ta birnin Leverkusen a kasar Jamus.

Lamarin ya faru ne ranar Talata, a unguwar ChemPark, wacce take zama wani sansani na kamfanonin sinadarai a birnin da ke Yammacin kasar.

An ga hayaki na tashi a sararin samaniya, lamarin da ya jawo hankalin hukumomi suka gargadi makwabtan unguwar su zauna a gaidajensu saboda fargabar fuskantar mummunar barna.

Rahotanni sun ce an sami fashewar ne da misalin karfe 07:40 na safe a agogon GMT, kuma ta yi sanadin tashin gobara a unguwar.

Hukumomin birnin sun ce fashewar ta samo asali ne daga wasu tankunan adana sinadarai, inda mutum 16 suka ji raunuka.

Har yanzu dai babu cikakkun bayanai kan musabbabin fashewar wacce kuma ta haifar da gobara, ko da yake an sami nasarar kasheta daga bisani.

Tuni dai aka girke jami’an ’yan sanda, ma’aikatan kwana-kwana, hilkwaftoci da kuma kuma motocin asibiti domin ayyukan ceto a yankin.

Sama da kamfanoni 30 ne dai suke da matsuguni a unguwar.