✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 5 sun mutu a rikicin kungiyar asiri

Jami'an tsaro sun cafke mutum uku da ake zargin na da hannu a rikicin.

Akalla mutum biyar ne suka rasa rayukansu a wani rikicin ’yan kungiyar asiri a Jihar Binuwe.

An kashe mutum hudu na farko ne a garin Gboko na Karamar Hukumar Gboko a jihar, dayan kuma aka kashe shi a Mukurdi, babban birnin Jihar, duk a ranar Alhamis.

Mazauna garin Gboko sun bayyana cewa rikicin ya faro ne daga daren ranar Talata zuwa safiyar Laraba, bayan wasu kungiyoyin asiri biyu sun kaure da fada a tsakaninsu.

Bayanai sun bayyana cewa an kashe mutum na farko a daren ranar Talata a yankin Gbar-Mkar, na hudun kuma aka kashe shi da safiyar ranar Laraba.

Wani mazaunin yankin ya ce da misalin karfe 1 na dare bayan ya fito ne ya hangi wasu mutane kusan su 20 da adda suna saran wani mutum.

Ya kara da cewa bayan sun kashe mutumin sai suka shiga gidajen makwabtaka suka kashe mutumin sannan suka sace musu dukiyoyi.

“Da muka fito da safe mun riske gawar wani dalibin Kwalejin Akperan Orshi, wannan ya sha saran adda,” cewar wanda ya gane wa idon nasa.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce tuni ’yan sanda suka cafke mutum uku da ake zargi da hannu a rikicin.

“Tabbas lamarin ya faru kuma mutum uku da ake zargin suna da hannu a rikicin sun shiga hannu, tuni kuma aka fara gudanar da bincike,” a cewar Anene.