✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 53 sun nitse a ruwa yayin bikin addinin Hindu a Indiya

Mutanen sun mutu ne rafuka daban-daban na jihar Bihar

Akalla mutum 53 ne suka nitse a rafuka daban-daban a yankin Bihar na kasar Indiya yayin bikin Chhath Puja na mabiya addinin Hindu a ranar Laraba.

Kafafen yada labarai da ke yankin sun rawaito cewa wadanda lamarin ya shafa sun nitse ne a wurare daban-daban yayin bikin da aka shafe yini hudu ana gudanarwa.

Rahotanni sun ce akalla mutum 18 ne suka mutu a ranar karshe ta bikin.

Gwamnan Lardin Bihar, Nitish Kumar, ya nuna alhininsa kan iftila’in, kana ya ba da sanarwar tallafin Dala 4,833 kwatankwacin Rufi 400,000 na kudin kasar, ga ahalin kowanne daga cikin marigayan.

Indiya kan gudanar da bikin Chhath Puja ta hanyar ziyartar rafuka a sassa daban-daban tare da jefa furanni a cikinsu.

Haka nan, sukan yi wanka a cikinsu don neman kariya da rahamar ababen bautansu.

(NAN)