✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 6 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi

Mutum shida ne suka mutu sakamakon hatsarin

An tabbatar da mutuwar wasu mutum shida, sannan wasu biyu sun jikkata sakamakon hatsarin motar da ya auku a kauyen Kwara da ke Karamar Hukumar Bogoro ta Jihar Bauchi.

Hatsarin, inji Shugaban Kungiyar Masu Motocin Haya (NURTW) na reshen Bogoro, Bauchi Yakubu, ya auku ne sakamakon kokarin kauce wa rami da direban motar ya yi.

Lamarin, a cewarsa ya sa motar ta saki hanya ta wuntsila ta fada rami da misalin karfe 5:00 na Asuba.

Ya ce, motar wadda kirar J5 ce, ta dauko mutane da shanu ne daga Taraba da nufin zuwa Kasuwar Mararaba a garin Liman Katagum.

Bayanai sun ce a nan take wasunsu suka mutu, wasu kuma bayan da aka dauke su zuwa asibiti rai ya yi halinsa.

“Gawarwakin na can a ajiye a Babban Asibitin Bogoro,” inji Yakubu.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC) na Jihar, Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar hatsarin.