✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 7 aka kashe, aka kona gidaje 250 a harin Miango

’Yan bindigar sun yi awon gaba da kadarori bayan shafe awa hudu suna barna.

Hukumomi a Jihar Filato sun ce mutum bakwai ne aka gano an kashe tare da kona gidaje 250 a sabon rikicin da ya barke a yankin Masarautar Miango da ke jihar.

Kungiyar Ci Gaban Yankin Iregwe da ke Jihar ta sanar a ranar Lahadi cewa ’yan bindigar da suka kutsa yankin sun lalata gonaki sama da 40 baya ga mutanen da suka kashe da kuma gidajen da suka kona a harin na ranar Asabar da dare.

Kakakin kungiyar na Kasa, Davidson Malison, ya ce, “Maharan da suka shafe kusan awa hudu suna cin karensu babu babbaka sun kona gidaje 250 a unguwannin Zanwra da Nche-Tahu da Rikwe-Rishe A da Rikwe-Rishe B da Ri-Dogo da kuma Nchu-Nzhwa, duk a Jebbu-Miango da ke Masarautar Miango.

“An kashe mutum bakwai, wasu da dama kuma an kai su asibiti suna samun kulawa, sannan an lalata gonaki sama da 40 tare da yin awon gaba da kadarori daga gidaje,” inji sanarwar.

Malison ya bayyana takaici game da abin da ya faru, sannan ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a yankin.

Da yake tabbatar da faruawr lamarin, Jami’in Hulda da Jama’a na ’yan sandan Jihar Filato, ASP Uba Oga ya ce tuni Runduar ’Yan Sandan Jihar ta tura jami’anta domin tabbatar da doka da oda a yankin.

“Muna kokarin shawo kan lamarin, mun kuma tura karin jami’ai. Ana bincike domin kamo wadanda suka aikata laifin su fuskanci hukunci,” kamar yadda ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN).