✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 7 sun rasu, 12 sun ji rauni a hatsarin mota

Hatsarin ya faru da sanyin asubahin ranar Talata.

Mutum bakwai sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota a kan hanyar Ayekale zuwa Ilorin-Bode Saduu a Jihar Kwara.

Hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce kima da wata mota kirar Toyota Bumper, mai lamba ZAR600XY ke yi.

Hatsarin da ya auku da misalin karfe 4 na asubahin ranar Talata ya lakume rayukan bakwai daga cikin fasinjoji 19 da ke cikin motar, mutum 12 kuma suka ji rauni.

Jami’an hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) reshen jihar, sun mika mutanen da hatsarin ya ritsa da su a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin don ba su agajin gaggawa.

Ko da Aminiya ta tuntubi Kwamandan hukumar, Jonathan Owoade, game da hatsarin, ya tabbatar da mana da faruwar hatsarin, sannan ya ja hankalin mutane da su guji yin tafiya a cikin dare domin hakan na da hatsari.

“Mun gano motar na gudu ne kuma ta samu matsalar birki, wanda hakan ne ya haifar da hatsarin.

“Shawarar da zan bayar shi ne mutane su guji yin tafiyar dare, saboda hatsari kan faru cikin sauki idan ana tukin dare, sannan babu wanda zai fito cikin dare ya ce zai ba wa wani taimako,” a cewarsa.