✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 700,000 ke kashe kansu a duk shekara —WHO

Yawancin masu kashe kansu matasa ne masu shekara 15 zuwa 29, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce sama da mutane 700,000 ne ke kashe kansu duk shekara a fadin duniya.

Wakilin WHO a Najeriya, Walter Kazadi Mulombu, ya ce kashi 77 cikin 100 na masu kashe kan nasu na yin haka ne saboda matsakaici ko karamin karfin tattalin arziki.

Wakilin na WHO ya bayyana hakan ranar Lahadi, cikin wata sanarwa da ya fitar, domin zagayowar ranar tunawa da ‘Matakan Kiyaye Aukuwar Kashe Kai ta Duniya’.

A cewarsa, a duk lokacin da wani ya kashe kansa, akwai wasu makamantansa 20 da ke aikatawa ko suke yunkurin aikatawa a daidai lokacin a wasu wuraren.

“Kashe kai ne sanadi na hudu a duniya da aka fi mutuwa ta hanyarsa, musamman a tsakanin matasa masu shekaru 15 zuwa 29.

“Kashe kai abin tashin hankali ne ga iyalin mamacin da gwamnati da kasa baki daya.

“Kuma abu ne da za a iya dakatar da shi ta hanyar hakuri da bayar da misalai da kuma shawarwari”, in ji shi.

Ana dai gudanar da bikin tunawa da ranar ce a dukkanin ranakun 10 ga watan Satumba.