✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 8 sun nitse a ruwa a Jigawa

Biyar sun kife ne a kwalekwale, uku kuma suka nitse a ruwa

Mutum takwassun rasa rayukansu a sanadiyyar kifewar kwalekwale da kuma nitsewa a ruwa a kananan hukumomin Gwaram da Kaugama da ke jihar Jigawa.

Rahotanni sun ce mutum biyar dai sun rasu ne a kauyen Martaba da ke karamar hukumar Gwaram, inda aka sami nasarar ceto hudu daga cikinsu.

A wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar, DSP Lawan Shi’isu Adam, kwalekwalen ya kife da mutanen ne yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga masallaci.

“Mutane hudu, da suka hada da wani mai shekara 60 mai suna Barkeji, sun tsira da rayukansu inda aka samu ceto su da ransu,” inji Kakakin.

Ya kuma ce a sanadiyyar gudunmawar da wasu masunta suka kai, an sami gawawwaki biyar da suka hada da wani dattijo mai suna Lukateru mai shekara 60 da Musa mai shekara 50 da Sale mai shekara 50 da Alhaji Shuaibu mai shekara 60 da Dogo mai shekara 50, dukkansu mazauna garin Darazau da ke Jihar Bauchi.

Ya kara da cewa, tuni an mika gawawwakin ga iyalai da yan uwan su domin yi musu jana’iza.

A wani labarin kuma, wasu yara mata uku, sun rasu a sakamakon nitsewa a ruwa a kauyen Faskarau da ke garin Ja’e a karamar hukumar Kaugaman ta jihar Jigawan.

Yaran sun hada da Maryam Salisu mai shekara 10 da Bahayura Lawan, ita mai shekara 10 da kuma Lawisa Sule mai shekara  takwas a duniya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar tsaro ta NSCDC, CSC Adamu Shehu, ya fitar ranar Litinin, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na safiyar Litinin, yayin da suka je wanki a rafi.

Ya ce an kai gawarwakinsu babban asibitin Kaugama, inda likita ya tabbatar da rasuwarsu.

Bincike ya nuna cewar, yaran, bayan sun gama wankin nasu ne suka yanke shawarar yin wanka, lamarin da ya jawo rasa rayukansu.

Mazauna yankin sun tabbatar da cewar shekaru 20 da suka gabata, an taba samun irin wannan iftila’in inda yara uku mata suka rasu.

Tuni aka yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada bayan mika gawarwakinsu ga iyalansu.

A nasa bangaren, babban kwamandan rundunar ta NSCDC a jihar, Musa Alhaji Mala ya jajanta wa iyalan mamatan, gami da jan hankalin iyaye da su kula wajen tura yara rafi, musamman a wannan lokacin da ake fama da ambaliyar ruwa a fadin Jihar.