✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 8 sun rasu, 5 sun jikkata a hanyar Minna-Katsina

Mutum takwas sun rasu, biyar sun jikkata a hatsarin mota a hanyar Minnna zuwa Katsina.

Mutum takwas sun rasu, wasu biyar sun samu raunuka a wani hatsarin mota a yankin Bonkwai na Jihar Neja.

Hatsarin na daren Asabar ya auku ne a yayin da motar, kirar Sharon, mai dauke da mutum 13, take hanyarta ta zuwa Katsina daga Minna.

Hukumar Kula da Hadurra ta Kasa (FRSC) ta ce hatsarin ya faru ne bayan tayar motar ta yi bindiga, a daidai Kwana Bokwai da ke hanyar Minna zuwa Lambatta.

Jami’in Hukumar mai kula da yankin Lambata, Babatunde Onemola,  ya ce mutum bakwai sun mutu ne a nan take, dayan kuma a Asibitin Tarayya da ke Gawu Babangida.

Ya ce mutum biyar din da suka samu raunuka kuma suna samun kulawa a asibiti.