✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 9 sun mutu a turereniyar wajen kallon waka a Guatemala

Daga cikin wadanda suka mutun har da kananan yara

Akalla mutum tara ne suka mutu, wasu 20 suka jikkata sakamakon wata turereniyar da aka yi a wani dandalin rawa da ke yammacin Guatemala.

Kafofin yada labaran kasar sun rawaito cewa lamarin ya ritsa da mutanen ne yayin da suke kokarin barin dandalin, bayan kammala kallon wasan mawaka ranar Alhamis.

Ma’aikatan ba da agajin gaggawa sun je da motocin daukar marasa lafiya harabar, in da aka kwashe su zuwa asibiti, kamar yadda kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta bayyana a shafinta na Twitter.

Taron mawakan dai an gudanar da shi ne domun murnar zagayowar ranar samun ’yancin kan kasar.

Wata mata da ta halarci taron mai suna Nancy Queme ta shaida wa manema labarai cewa santsin tabo ne ya sanya mutane suka rika zamewa, sakamakon mamakon ruwan saman da aka tafka a ranar.

Mutanen da suka jikkata dai an kai su asibiti inda suke karbar magani kamar yadda ma’aikatan kashe gobara na yankin suka bayyana a shafin Twitter.

To sai dai Jaridar Guatemala Prensa Libre ta ruwaito cewa, kawo yanzu hukumomin kasar ba su bayyana sunayen wadanda suka mutu ba, sai dai kafofin yada labaran kasar  sun ce cikin wadanda suka mutun har da kananan yara biyu.