✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 9 sun mutu a turmutsitsin murnar Sabuwar Shekara a Uganda

’Yan sanda sun ce sakaci na daga dalilan da suka haifar da iftila'in.

Akalla mutum tara sun mutu sakamakon turmutsitsin a wajen taron bikin murnar shiga Sabuwar Shekara a Kampala, babban birnin Uganda ranar Lahadi.

Lamarin ya auku ne bayan kammala wasan wuta inda mutum biyar suka mutu nan take wasu da dama kuma suka jikkata.

’Yan sandan yankin sun ce an samu karin wadanda suka mutun ne daga cikin wadanda aka kwashe su zuwa asibiti.

Duk da cewa babu cikakken bayani kan yanayin shekarun wadanda suka rasa rayukan nasu, amma ’yan sanda sun ce galibinsu matasa ne.

A cewar ’yan sandan, sakaci daga bangaren mahalarta taron na daga cikin dalilan da suka haifar da iftila’in.