✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 9 sun rasu bayan motarsu ta fada cikin Dam a Kano

Har yanzu ana neman gawar mutum daya a ciki

Akalla mutum tara ne aka tabbatar da rasuwarsu bayan wata mota kirar Golf ta fada Dam din Fada da ke kan hanyar Kano zuwa Katsina.

Sai dai an samu nasarar ceto mutum uku daga cikin ruwan a hatsarin da ya faru a karshen mako.

Da yake tabbatar da faruwar hatsarin, Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce hukumar ta sami kiran gaggawa ne daga wani daga yankin.

Ya ce, “Wani mai suna Ali Mai Faci ne ya kira mu wajen misalin karfe 6:00 na yamma, cewa wata mota da ke tafe daga hannun Kano ta doshi hanyar Katsina ta fada cikin Dam din.

“Jami’anmu da wasu masunta sun ceto mutum uku a raye, sai kuma mutum tara da ba sa cikin hayyacinsu da muka garzaya da su Babban Asibitin Gwarzo, inda likita ya tabbatar da rasuwarsu,” inji Kakakin.

Sai dai ya ce za su ci gaba da bincike kasancewar har yanzu akwai gawar mutum daya da suke nema a cikin ruwan.

Dam din da lamarin ya faru dai yana cikin Karamar Hukumar Gwarzo ta jihar Kano.