✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 90 sun warke daga COVID-19 a rana guda a Legas

Mutum 90 ne aka sallama a ranar Juma’a 12 ga watan Yuni bayan sun warke daga cutar COVID-19 a jiha Legas. An sallami mutanen ne…

Mutum 90 ne aka sallama a ranar Juma’a 12 ga watan Yuni bayan sun warke daga cutar COVID-19 a jiha Legas.

An sallami mutanen ne sun koma cikin iyalensu daga cibiyoyin killace masu cutar guda bakwai a jihar.

Mutum 1,137 nan yanzu suka warke daga cikin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a jihar Legas inda cutar ta fi kamari a Najeriya.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce mutanen da aka sallama din bayan gwaje-gwaje sun tabbatar da sun warke sun hada da mata 30 da maza 60.

Sanwo-Olu ya jinjina wa ma’akiatan lafiya kan irin jajircewar da suke nunawa wurin yaki da cutar ta COVID-19.

Ya kuma bukaci jama’ar jihar da su ci gaba da bayar da hadin kai ta hanyar bin matakan kariya wanda shi ne babban mafita daga kamuwa da cutar mai yaduwa.