✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum dubu 100 sun tsere zuwa Nijar kan hare-haren Boko Haram a Borno

Wannan sabon hari na zuwa ne cikin kasa da sa’a 24 bayan aukuwar makamancinsa a ranar Talata.

Akalla mutum dubu 100 ne a ranar Laraba suka tsere daga garin Damasak na Jihar Borno zuwa Jamhuriyyar Nijar sakamakon jerin hare-haren mayakan Boko Haram.

Majiyoyin gwamnatin sun ce akalla mutum 10 aka kashe sannan da dama sun jikkata yayin da wasu dubbai suke watangariri a cikin jeji.

Rahotanni sun bayyana cewa, maharan sun kona daruruwan gidaje da shaguna da gine-ginen gwamnati da kuma ofishin ’yan sanda.

Wannan mummunan hari da ya auku ranar Laraba a Damasak, shi ne karo na shida cikin makonni biyu, inda cikin kwanaki hudu da suka gabata sojoji ke ci gaba artabun kwato garin daga hannun yan ta’adda.

Wannan sabon hari na zuwa ne cikin kasa da sa’a 24 bayan aukuwar makamancinsa a ranar Talata.

Yayin harin da ya auku a ranar Talata, rahotanni sun bayyana cewa, sojoji sun fatattaki mayakan amma sun yi wa garin mummunar illa da ba za ta misaltu ba.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Asabar, 10 ga watan Afrilu ne mayakan Boko Haram suka kai hari garin Damasak, inda suka kashe mutum shida ciki har da mata biyu da sojoji uku.

Mata, wasunsu masu juna biyu wasu kuma goye da jarirai da kananan yara na biye da su a baya, su ne wadanda wannan hari ya fi jefa wa cikin mawuyacin hali duba da yadda suka fito daga gidajensu babu shiri domin tseratar da rayukansu.

A halin yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar sojin da ta bayar da shaidar halin da ake ciki a garin mai fuskantar hare-haren mayakan Boko Haram kusan shekara 11 da suka gabata.

Sai dai wasu majiyoyi masu karfi sun tabbatar da cewa mayakan sun kafa tutarsu a cikin garin kuma ba su da shirin fita.

Garin Damasak wanda ke da tazarar kilomita 188 tsakaninsa da birnin Maiduguri, ya yi iyaka da Jamhuriyyar Nijar da wasu Kananan Hukumomi a gabar Tafkin Chadi.