✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum fiye da 1,300 sun mutu a girgizar kasar Haiti

Ana hasashen wata guguwa da ake kira ‘Tropical Storm Grace’ ta sake lullube kasar.

Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasa a kudancin kasar Haiti ya haura mutum 1,300, a cewar wata sanarwa da Hukumar Kare Fararen Hula ta Kasar ta fitar a ranar Lahadi.

Ma’aikatar Binciken Yanayin Kasa ta Amurka ta ce, inda girgizar kasar ta auku na da nisan kilomita kimanin 160 daga tsakiyar Port-au-Prince babban birnin kasar Haiti da ke da cinkoson jama’a.

Haka kuma, ta ce girgizar kasar ta ranar Asabar ta fi tasiri ne a wani wuri mai nisan kilomita 12 da garin Saint-Louis du Sud, inda aka kiyasta cewa ta jawo asara ta kusan Dala biliyan takwas.

A baya alkaluman da mahukunta suka fitar sun bayyana cewa, kimanin mutum 724 aka tabbatar da mutuwarsu yayin da 2,800 suka jikkata a girgizar kasar da ta rusa dubban gine-gine.

Haka kuma, alkaluman sun yi nuni da cewa ana tsammanin adadin wadanda suka mutu zai haura haka yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da neman wadanda suka tsira.

Kawo yanzu ba a tabbatar da hakikanin alkaluman barnar da girgizar kasar ta haddasa ba wacce ta janyo asarar dubban gidaje da kayayyakin more rayuwa.

Ma’aikatan agaji da masu bayar da gudunmuwa a kasar sun dukufa wajen kokarin ceto mutanen da suka tsira da rayukansu da kuma zakulo gawarwakin mutanen da suka mutu daga karkashin baraguzan gine-gine.

Tuni dai Firaministan Kasar, Ariel Henry ya sanya dokar ta-baci ta tsawon wata guda bayan aukuwar girgizar kasar.

Aikin ceto da Kungiyar Agaji ta Duniya Red Cross ke gudanarwa ya mayar da hankali ne kan yankin da ke kusa da garuruwan Jeremie da Les Cayes inda abin ya fi shafa, kuma an tanadi kayan agaji da akalla mutane 4,500 za su amfana.

Sai dai ana zargin matsalar da kasar Haiti ke fuskanta a halin yanzu na iya ninkuwa yayin da aka yi hasashen wata guguwa da ake kira ‘Tropical Storm Grace’ ta sake lullube kasar.

Haiti, wacce ake ganin ita ce kasa da talauci ya fi yi wa katutu a Yammacin Duniya, a yanzu haka tana kokarin farfadowa daga makamanciyar musibar girgizar kasar da ta afka mata a shekarar 2010.

Bayanai sun ce a ranar 12 ga Janairun 2010 ce girgizar kasa mai karfin maki 7.0 ta auku a kasar wacce ta yi ajalin mutane 220,000 sannan ta raba mutane miliyan daya da matsugunansu.

Girgizar kasar ta ranar Asabar na zuwa ne yayin da Haiti ke fama da rikicin siyasa tun bayan kisan shugabanta,  Jovenel Moise a watan Yulin da ya gabata.