✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum miliyan 1.2 ne ke fama da yunwa a Mali

Bincike ya nuna yadda mutane da yawa a kasar ke kasa sayen kayan masarufi saboda tsananin tsada.

Akalla mutum miliyan 1.2 ke fama da matsananciyar yunwa a kasar Mali tun daga shekarar da ta gabata.

Gamayyar kungiyoyin agaji 22 ne suka bayyana alkaluman mutanen.

Kungiyoyin sun ce matsalar tsaro da ta addabi Malli da kuma bullar annobar COVID-19 a 2020 ne musababbin karuwar mutanen da ke fama da yunwa a kasar.

Yunwar da ake fama da ita a halin yanzu ita ce mafi muni tun bayan wanda aka samu a farkon rikicin Mali na 2012, kamar yadda kungiyar FONGIM ta bayyana.

Rashin abincin da ruwan sha ya jefa kusan mutum miliyan uku cikin matsananci hali, musamman a yankunan Timbuktu da Ségou.

Matsalolin da ke addabar kasar a halin yanzu, sun sa kayayyakin masarufi yin tashin gwauron zabo da kashi 22 cikin 100.

Lamarin ya jefa magidanta da yawan gaske cikin tasku na gaza sayan kayan abinci a kasar.