✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum miliyan 15 na ta’ammali da kwaya a Najeriya — Buba Marwa

Sabon Shugaban Hukumar NDLEA mai Yaki da Ta’ammali da Fataucin Miyagun Kwayoyi a Najeriya, Birgediya Janar Buba Marwa, ya sanar cewa a shekarar 2018 binciken…

Sabon Shugaban Hukumar NDLEA mai Yaki da Ta’ammali da Fataucin Miyagun Kwayoyi a Najeriya, Birgediya Janar Buba Marwa, ya sanar cewa a shekarar 2018 binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa akwai kimanin ’yan Najeriya miliyan 14.3 da ke ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Birgediya Janar Buba Marwa wanda ya fara aiki a matsayin sabon shugaban Hukumar a wannan mako, ya bayyana hakan ne a jawabinsa na farko da ya fitar a hedikwatar NDLEA da ke birnin Abuja.

Ya bayyana damuwa kan yadda ake ci gaba da samun karuwar masu ta’ammali da miyagun kwayoyin wanda a cewarsa galibinsu ’yan tsakanin shekara 15 zuwa 64 ne.

Tsohon gwamnan soja na jihohin Borno da Legas, ya lashi takobin cewa hukumar a karkashin jagorancinsa za ta jajirce wajen kawo ingataccen sauyi da fadada ayyukanta.

Kazalika, ya ce, zai jajirce wajen ganin rage yawan ta’ammali da kwayoyi sannan ya sha alwashin inganta jin dadin ma’aikatan hukumar.

“Ina so na gargadi duk wadanda ke aikata wannan mummunar dabi’ar ta shigowa, fitarwa, nomawa, sarrafawa, kerawa, fatauci, sayarwa da shan miyagun kwayoyi da su dakata haka nan ko kuma su zama cikin shiri fuskantar fushin Hukumar NDLEA,” inji shi.

“Ina so na baku tabbacin cewa za a ba wa walwala da jin dadinku muhimmanci domin kuwa za mu kawo karshen matsalolin jinkirin karin matsayi, bayar da horo, da kuma sauran abubuwar da suka danganci ingancta walwala da jin dadinku.”

Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Birgidiya Janar Buba Marwa a matsayin sabon Shugban hukumar ta NDLEA.

Kafin nadin nasa, Buba Marwa shi ne shugaban Kwamitin da ke ba Shugaban Kasa Shawara kan Yaki da Miyagun Kwayoyi (PACEDA) tsakanin shekarun 2018 zuwa 2020.