✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum miliyan 2.5 sun yi rajistar jam’iyyar APC a Kano – Ganduje

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya ce kawo yanzu an yi wa akalla mutum miliyan 2.5 rajistar jam’iyyar APC yayin sabunta rajistar ’ya’yan…

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya ce kawo yanzu an yi wa akalla mutum miliyan 2.5 rajistar jam’iyyar APC yayin sabunta rajistar ’ya’yan jam’iyyar da ke ci gaba da gudana a fadin kasar.

Ganduje wanda ake yi wa lakabi da Khadimul Islama, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin taron masu ruwa da tsaki karo na shida da aka gudanar a dakin taro na ‘Africa House’ da ke fadar Gwamnatin Kano.

Ya yaba wa kokarin dukkan masu ruwa da tsakin da suka taka rawar gani wajen tabbatar da cewa jihar Kano ta yi fice a aikin sabunta rajistar mambobin jam’iyyar.

“Kowannen mu yana sane da yadda aka karar da rukunin farko na katin rajista na mutum 100 da aka aika kowace rumfar zabe sannan a yanzu da aka sake aika rukuni na biyu na kati 200 ana neman kararwa saboda yadda mutane ke tururuwar zuwa a yi musu rajista.”

A kokarin da yake yi a jiharsa kamar yadda Gwamna Ganduje ya bayyana, shi ne bunkasa jam’iyyar domin karfinta ya ninku, “don a yanzu mambobin jam’iyyar sun doshi miliyan 3 zuwa 4 a Jihar,” in ji shi.

Ya kara da cewa, kasancewar jihar Kano tana da rumfunan zabe 8,090, shelkwatar jam’iyyar APC ta tanadar wa jihar katin rajista na mutum 100 a duk rumfa, amma cikin kankanin an karar da su kamar yadda Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masaurautun Gargajiya Murtala Sule Garo ya tabbatar.