✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum miliyan 7 ne suka yi Umarah a 2022 – Saudiyya

A 2022 aka fara barin masu bizar da ba ta Umarah ba damar yin Umarah a Saudiyya.

Ma’aikatar Aikin Hajji da Umarah ta kasar Saudiyya ta ce kimanin mutum miliyan bakwai ne suka yi aikin Umarah a shekarar 2022.

Wannan adadin a cewar ma’aikatar ya hada da baki su miliyan hudun da suka samu izinin shiga kasar domin Hajjin Umarah.

Kamfanin dillancin labarai na SPA ya rawaito a ranar Alhamis cewar, Ma’aikatar ta yi amfani da harsuna 14 wajen isar da muhiman bayanai da suka shafi addini da kiwon lafiya da sauransu ga maniyyatan yayin zamansu a kasar.

Kazalika, ta ce ta tabbatar da maniyyatan sun samu kulawar da ta dace wajen gudanar da harkokinsu da suka hada yanka da ziyartar wurare da sauransu.

Ta kara da cewa, ta sahale wa masu rike da biza daban-daban ibadar Umarah a wannan shekarar.

Ta ce a 2022 ne ta kyale masu bizar yawon  shakatawa suka yi Umarah yayin zamansu a kasar, wanda hakan shi ne karon farko da irin hakan ta faru.