✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum miliyan uku sun yi aikin Umara a watan Ramadana

Mutum sama da miliyan uku ne suka gudanar da aikin Umara a Masallacin Harami a watan Ramadana na bana. Shafin Haramain Sharifain na mahukunta masallatan…

Mutum sama da miliyan uku ne suka gudanar da aikin Umara a Masallacin Harami a watan Ramadana na bana.

Shafin Haramain Sharifain na mahukunta masallatan harami na birnin Makkah da Madina ne ya wallafa hakan ranar Litinin a shafinsa na Twitter.

A bara ce Saudiyya ta ba da lamunin dawo da ibadar Umara kamar yadda aka saba yi a baya.

Sai dai an samu sauye-sauyen al’amura sakamakon bullar annobar  cutar Coronavirus da ta dagula al’amura a duk wani kwararo da sako na duniya.

Musulmi yayin gudanar da ibada a masallacin Harami
Wani sashe na Masallacin Harami da ke Makkah
Musulmi yayin gudanar da ibada a wani sashe na masallacin Harami na Makkah

Miliyoyin Musulmi ne bisa al’ada ke zuwa ibdar Umarah duk watan Ramadan, inda a yanzu an samu ci gaba bayan sassauta dokokin dakile yaduwar cutar.

Alkaluman da mahukunta Saudiyya suka fitar sun nuna cewa mutum 6,979 cutar coronavirus ta kashe inda a halin yanzu an yi wa kimanin mutum miliyan rigakafin cutar.