✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum na farko ya kamu da kwayar cutar Omicron a Saudiyya

Karon farko ke nan da aka samu bullar nau'in cutar a fadin yankin kasashen Larabawa

An gano mutum na farko da ke dauke da kwayar Omicron na cutar COVID-19 a kasar Saudiyya.

A ranar Laraba hukumomin lafiya na Saudiyya suka gano mai dauke da kwayar cutar, wanda shi ne na farko a yankin kasashen Laraba.

Ma’aikatar lafiya ta kasar ta ce tuni aka killace wanda aka gano da cutar, a yayin da jami’anta suke ci gaba da ba shi kulawa.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Saudiyya, SPA ya ambato Hukumar Lafiya ta kasar na cewa an gano kwayar cutar ce a jikin wani dan kasar da ya dawo daga wata kasa a Kudancin Afirka.

Hukumar Lafiyar Saudiyya dai ba ta bayyana kasar da mutumin ya ziyarta ba.

Ko kafin a gano kwayar cutar, Saudiyya ta haramta tafiye-tafiye zuwa wasu kasashen Afirka saboda kauce wa yaduwar kwayar cutar ta Omicron.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) dai ta bayyana Omicron a matsayin abin damuwa, gami da fargabar ta fi sauran nau’ikan cutar COVID-19 saurin yaduwa.