✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum na uku ya rasu a hatsayin jirgi na Legas

Mutum na uku daga cikin wadanda hatsarin jigin saman ranar Juma’a a Legas ya ritsa da shi ya rasu, bayan awanni da kai shi asibiti.…

Mutum na uku daga cikin wadanda hatsarin jigin saman ranar Juma’a a Legas ya ritsa da shi ya rasu, bayan awanni da kai shi asibiti.

Tun bayan faduwar jirgin mai saukar ungulu a yakin Ikeja matukansa biyu suka rasu yayin da aka garzaya da mutum na uku da ke cikin jirgin zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas (LASUTH).

Shaidu sun ce da zuwa da shi an wuce da shi bangaren tiyata ne saboda yana cikin tsananin mawuyacin hali.

Rahotanni sun ce daga baya shi ma ya cika duk da dai hukumomi ba su kai ga sanarwa ba.

“Abin takaici yanzu mutum uku ke nan suka rasu, da suka hada a matukin jirgin, Kyaftin Chika Prudence Ernest da injiniyan jirgin Clement Ndiok”, inji majiyarmu.

Tuni dai Hukumar Binciken Hadurran Jiragen Sama (AIB) ta dauki akwatin nadar bayanan jirgin domin fara binciken musabbabin hatsarin na ranar Juma’a.

Gabanin azahar ne jirgin mai dauke da mutum uku ya fado a cikin wasu gidaje.

Hukumomin agaji da kwanakwana a Jihar Legas, tun da farko sun tabbatar da faruwar lamarin da kuma wadanda abin ya ritsa da su.