✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum tara ne ke neman sarautar Sarkin Katagum

Wata majiyar Fadar Katagum ta tabbatar wa wakilin Aminiya cewa masu neman sarautar sun mika takardunsu ne jim kadan da aka kammala addu’ar kwana uku…

Wata majiyar Fadar Katagum ta tabbatar wa wakilin Aminiya cewa masu neman sarautar sun mika takardunsu ne jim kadan da aka kammala addu’ar kwana uku ta rasuwar marigayi Mai martaba Sarkin Katagum Alhaji Muhammadu Kabiru Umar.

Wani babban jami’i a fadar da ya nemi a sakaye sunansa, ya ce fitattatu daga cikin wadanda suke neman sarautar su ne Alhaji Baba Kabir Umar, babban dan marigayi Sarki Kabir Umar da Alhaji Lele Mukhtar da Birgediya Janar Yakubu Mu’azu, tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato da kuma Ambasada Adamu Bulkachuwa,

Haka kuma Aminiya ta ji cewa bayan su akwai mutum biyar da a ranar Talata da yamma suka mika takardunsu kuma ana sa ran masu zaben Sarkin Katagum da suka hada da Waziri da Galadima da Liman da Makama da Madaki za su zauna su tantance su zabi mutum uku su mika wa Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Mohammed Abdullahi Abubakar domin ya dauki mutum guda daga cikinsu.

daya daga cikin masu zaben Sarkin ya shaida wa Aminiya cewa har zuwa yanzu ba su kai ga zama ba, balle su tantance masu neman, amma kowane lokaci za su iya zama. Kuma ya roki jama’a su taya su addu’ar Allah Ya yi musu jagora su zabi wanda zai zama mafi alheri ga al’ummar masarautar.

Ya ce jama’a su kwantar da hankalinsu domin dukan masu neman sarautar ’yan uwan juna ne, suna da zumunci a tsakaninsu kuma za su ci gaba da zumunci koda bayan an nada sabon Sarki.

Kuma ya musanta jita-jitar da ake yadawa ta kafafen sadarwar sada zumunta na zamani cewa an nada daya daga cikin wadanda suke neman sarautar.

Tun lokacin da aka samu labarin rasuwar Sarkin Katagum ake samun rade-radin cewa wadansu daga cikin ’ya’yan Sarkin da kuma jinin sarautar sun fara kamun kafa da neman addu’a a wajen bayin Allah da kuma ’yan uwa da abokan arziki domin neman dacewa da samun sarautar Sarkin na Katagum.

Masarautar Katagum, tsohuwar masarauta ce da aka kafa ta fiye da shekaru 210, kuma sarakuna goma sha daya ne suka yi mulkinta. Daga cikinsu akwai Malam Ibrahim Zaki wanda ya yi sarauta daga 1807 zuwa 1814 sai Sarki Sulaiman Adandaya daga 1814 zuwa 1816, sai Sarki Muhammad dankauwa daga 1816 zuwa 1846, sai Sarki Abdurrahman daga 1846 zuwa 1851, sai Sarki Abdulkadir na Farko daga 1851 zuwa 1868, sai Sarki Muhammadu Haji daga 1868 zuwa 1896, sai Sarki Abdulkadir na Biyu daga 1896 zuwa 1805,  sai Sarki Muhammadu Damamisau daga 1905 zuwa 1909, sai sarki Abdulkadir na Uku daga 1909-1947, sai Sarki Umaru Faruku daga 1947 zuwa 1980 sai kuma Sarki Muhammadu Kabiru Umar, Sarki na 11 wanda ya yi sarauta daga 1980 zuwa 2017. Yanzu Sarki na 12 ne ake sa ran za a nada don haye wannan muhimmiyar kujera.