✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutumin da ya fi kowa fama da kadaici a duniya ya mutu

Wani mutum da shi kadai ya rage daga kabilarsa, kuma ya rayu shi kadai tsawon shekara 25 a kasar Brazil, ya mutu.. Wata kungiyar kare…

Wani mutum da shi kadai ya rage daga kabilarsa, kuma ya rayu shi kadai tsawon shekara 25 a kasar Brazil, ya mutu..

Wata kungiyar kare hakkin ‘yan kasar ce ta bayyana hakan a ranar Lititnin.

Wata hukumar kidayar kabilun kasar Brazil din da aka dora wa alhakin lura da shi, ta ce an tsinci gawarsa ne a kan gadonsa.

Marigayin, mai suna Indio Tanaru, wanda aka fi sani da Tanarun Rami, shi ne mutum na karshe da ya rage daga kabilar da ya fito, kuma tilo da ke zaune unguwar Tanaru da ke jihar Rondonia a kasar.

Haka zalika kafin mutuwarsa shi ne mutumin da ya fi kowa kadaici a duniya.

‘Yan gwagwarmaya a kasar dai sun ce sauran mutane kabilarsa sun kare ne bayan makiyaya sun karkashe su a shekarar 1970-80, yayin da suke kokarin fadada matsugunansu a kasar.