✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutumin da ya je aikin Hajji a kafa daga Birtaniya ya isa Makkah

Kullum sai yi ya yi tafiyar kilomita 17.8 yana tura kurar guzurinsa a tsawon wata 11 inda ya bi ta kashashe 10 kafin ya isa…

Wani maniyyaci da ya tafi aikin Hajji a kafa daga kasar Birtaniya ya isa birnin Makkah na kasar Saudiyya inda za a sauke farali da shi a bana.

Adam Mohammed mai shekara 52 ya cika burinsa na zuwa aikin Hajji a kafa ne bayan ya yi tafiyar Kilomita 6,500 yana tura kurar guzurinsa, kullum kilomita 17.8 a tsawon wata 11 da kwana 29.

Adam wanda ya keta kasashe 10 kafin isarsa Saudiyya, ya ce: “Na yi matukar farin ciki da cikar wannan buri nawa da kuma irin gagaruwar tarba da kauna da mutanen Saudiyya da sauran kasashe suka nuna min.

“Hakika ina cike da shaukin ganin an yi aikin Hajji tare da ni saboda ba ni da wani buri a rayauwa da ya wuce shi.”

Ya bayyana haka ne a lokacin da dandazon alhzai da mutanen Saudiyya tare da ’ya’yansa mata biyu da suka je Hajji daga Birtaniya ta jirgin sama suka yi mishi wata gagarumar tarba a Masallacin A’isha da ke Makkah.

A tsawon wata 11 da kwana 26 da Adam Mohammed ya kwashe a hanya, a kullum yakan yi tafiyar kilomita 17.8 a kafa, har ya isa Masallacin Aisha da ke Makkah, inda ya yi wanka domin daukar harama a ranar 26 ga watan Yuni, 2022.

Kasashen da ya bi kuwa su ne: Netherlands da Jamus da Jamhuriyar Czech da Hungary da Romania da Bulgaria da Turkiyya.

Sauran su hada da Lebanon da Syria da Jordan har ya isa Kasar Saudiyya bayan ya ci kilomita 6,500 yana tafiya a kafa.

Adam Mohammed, bayan ya dauki harama jin kadan da isarsa Saudiyya. (Hoto: Arab News).

Abin da zan yi a Tsayuwar Arafat

Ya bayyana cewa idan Allah Ya kai shi ranar Tsayuwar Arafat, “Zan yi wa Allah godiya da ya ba ni ikon kammala wannan tafiya lafiya da cika min wannan buri nawa a kan lokaci.

“Hakika wannan tafiya ba karamin aiki ba ne, sai da na sarayar da komai saboda Allah.

“Abin da na shagaltu da shi shi ne karatun Al-kur’ani tun daga lokacin da aka sanya takunkumin COVID-19.

“Daga baya, wata rana sai kawai na ji ina son zuwa aikin Hajji a Makkah a kafa daga kasata — kuma na kasa hakura — sai kawai ya yanke shafarar tafiya.”

Yadda ya yi tafiyar

Adam ya ce ya shafe wata biyu yan shirye-shiryen wannan tafiya mai dimbin tarihi, tare da taimakon wata kungiyar kasar Birtaniya da kuma tallafin daga wasu daidaikun ’yan kasarsa, Birtaniya.

Maniyyacin, wanda asalinsa Bakurde ne daga kasar Iraki ya kama hanyarsa ta zuwa aikin Hajji a kafa ne a ranar 1 ga watan Agusta, 2021, daga gidansa da ke yankin Wolverhampton na kasar Birtaniya.

Ya kuma fito ne tare da guzurinsa mai nauyin kilogiram 250, wanda ya sanya a cikin wata kura.

“Gaskiya, ni da kaina na kera kurar, a cikinta kuma nake yin girki, nake cin abinci, nake kuma yin barci.”

Adam Mohammed da kurarsa, a hanyarsa ta zuwa aikin Hajji a kafa daga Birtaniya. (Hoto: Arab News).

Yanayin tafiyar

Da yake bayani game da yadda tafiyar tasa ta kasance, ya ce babu wata wahala da zai ce ya sha.

Abin da kawai zai iya kira a matsayin kalubale shi ne bambancin yanayin wuraren da ya bi a hanyar tasa ta zuwa Makkah.

“Babu wata babbar wahala, in banda ’yan wurare da ’yan sanda da jami’an gwamnatin kasashen da na bi sukan tsayar da ni sun tambayi dalilin shigowata kasarsu.

“Amma idan na yi musu bayani game da wannan tafiya tawa, sai su cika da mamaki,” inji shi.

Ya ce a kan hanyarsa kuwa, mutane sun yi ta ba shi gudunmmawa — daga masu zuwa musamman domin su tura mishi kura, sai masu ba shi abinci ko masaukin da zai huta.

Bayan isarsa kasar Saudiyya ne mahajjacin ya bayyana yadda tafiyar tasa ta kasance kai-tsaye ta shafukansa na YouTube da Instagram da TikTok, yana mai yada sakonnin zaman lafiya.

Kusan mutum miliyan uku ne suka so bidiyon nasa a TikTok, duk da ya bayyana cewa ya yi wannan tafiya ce domin ibada, ba don neman shuhura ba.