✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutumin da ya nemi kashe Limamin Masallacin Harami ya ce shi ne Mahadi

Mutumin da ya nemi kashe Limamin Masallacin Harami ya yi ikirarin zama Mahadi

Mutumin da ya yi yunkurin kashe Limamin Masallacin Harami da ke Makkah a lokacin da yake gabatar da hudubar Sallar Juma’a ya yi ikirarin cewa shi ne Mahadi.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Hukumar Kula da Masallatan Harami kuma Limamin Haramin Makkah, Sheikh Abdulrahman Sudais, ya nada sabon Kwamandan Rundunar Tsaron Masallacin Haramin Makkah, tare da ba da umarnin kara tsaurara matakan tsaro a Masallatan Harami.

Idan ba a manta ba, askarawan Saudiyya sun cafke wani mahari a lokacin da ya kai wa Limamin Masallacin Haramin Makkah, Sheikh Bandar Baleelah, hari da makami yana tsaka da huduba a ranar Juma’a, 21 ga Mayu, 2021.

Maharin, wanda ke sanye da haramin Umrah, ya fito daga cikin sahu ne a guje ya nufi mumbarin da Sheikh Baleelah ke gabatar da huduba, amma jami’an tsaro suka damke shi a dokin kofar mumbarin.

A lokacin bincike, mutumin mai shekara 40 wanda dan kasar Saudiyya ne ya bayyana musu ikirarinsa cewa shi ne Mahadi, wanda zai bayyana a karshen zamani.

Harin nasa shi ne na biyu da a cikin kimanin shekara 50 da aka kai wa limaman Masallacin na Harami daga masu ikirarin zama Mahadi.

Yunkurin kashe Limamin Harami yana huduba

Bayan Harin na ranar Juma’a shafin Masallacin Harami ya fitar da bidiyon yadda lamarin ya faru.

“Mutumin na dauke da makami a lokacin da ya nufi wurin da limamin ke gabatar da huduba,” inji sakon da masallacin ya fitar tare da bidiyon.

A cikin bidiyon an ga wani mutum sanye da Harami yana tsallaka sahu a guje, yana zuwa dokin kofar mumbarin limamin, sai askarawa suka tare shi suka cukwikuye shi, nan take suka yi awon gaba da shi.

Sheikh Sudais yana ganawa da sabon Kwamandan Rundunar Tsaron Masallacin Haramin Makkah. (Hoto: @hsharifain).

Tsaron Masallacin Harami

Gwamnatin kasar Saudiyya ta ba da muhimmanci ga tsaron Masallatan Harami da Limamansu, kasancewar ba karon farko ba ke nan da ake kai musu hare-hare.

Hare-haren da aka kai wa Limaman Masallacin Harami

Kimanin shekara 20 da suka gabata, wani mutum ya yi yunkurin daba wa Sheikh Abdulrahman Sudais wuka a lokacin da yake zaman Tahiyar karshe a lokacin da yake limanci a Masallacin Harami.

A 2011 kuma wani mutum ya ture daga daga cikin limaman Masallacin Harami, wato Sheikh Abdullahi Jahani, ya dauki makirfon ya yi ta ihu.

Kafin shi wani mutum ya taba neman kai wa Sheikh Ali al-Hudhaifi hari a yayin da malamin yake limancin Sallar Subahi.

Harin ’yan bindiga Masallacin Harami

Shekara 1979, ’yan bindiga kusan su 200, karkashin jagorancin Juhayman al-Utaybi, sun kai kazamin hari a Masallacin Harami a lokacin aikin Hajji, wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

A lokacin, bayan liman ya idar da sallah, sai Juhayaman da almajiransa suka tunkude shi suka kwace makirfon, suka fara jawabi da cewa Mahadi ya dawo.

Gabanin haka, sun riga sun shigo da makamansu a cikin makara; sai da ta kai ga an nemi dauki tare da shafa musu gas mai guba kafin a murkushe su.

An dauki kwanaki ana gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati, da mutanen da suka kai harin a lokacin aikin Hajji.

A karshe dai gwamnatin Saudiyya ta yanke wa Juhayaman da almajiran nasa hukuncin kisa.

Tun daga wannan lokaci kasar Saudiyya ke bayar da tsaro na musamman a Masallacin Harami da limamansa.