✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Mutumin da ya taso a Najeriya ya auri ’yar Donald Trump

Angon dai ya taso ne a birnin Legas na Najeriya

Tiffany Trump, ’yar tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, a karshen mako ta auri masoyinta wanda ya taso a Najeriya, Michael Buolos.

An yi bikin ne ranar Asabar a gabar ruwa ta Mar-a-Lago da ke birnin Florida a Amurka. Donald Trump da matarsa, Melania sun halarci bikin.

Michael Buolos dai, wanda iyayensa ’yan asalin kasashen Lebanon da Faransa ne ya tashi a birnin Legas na Najeriya.

Bayanai sun nuna ya zo Najeriya ne tun da kuruciyarsa, saboda a nan iyayensa suke kasuwanci. Ya yai karatu a makarantar American International School da ke Legas din.

Kazalika, Michael da ne ga Massad, Shugaban kamfanin SCOA da ke Najeriya, yayin da mahaifiyarsa, Sarah, ita ce ta kirkiri Kungiyar Masu Wasan Kwaikwayo ta Najeriya.

Ga wasu daga cikin kyawawan hotunan bikin da aka gudanar a Amurkan: