Mutumin da ya yi garkuwa da yaro a Kano zai bakunci hauni | Aminiya

Mutumin da ya yi garkuwa da yaro a Kano zai bakunci hauni

    Lubabatu I. Garba, Kano

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 5 da ke Sakateriyar Audu Bako ta yanke wa Ibrahim Ahmad Khalil hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin garkuwa da wani yaro mai suna Ahmed Ado tare da kashe shi.

Tun farko Lauyan Gwamnati kuma mai gabatar da kara, Barista Lamido Abba Soron Dinki ne ya gabatar da wanda ake zargin a gaban kotun, inda ya ce a shekarar 2019 ne wanda ake zargin ya sace yaron a Unguwar Karkasara, kuma ya nemi kudin fansa daga iyayensa na Naira miliyan 20.

Sai dai kafin a biya kudin, wanda ake zargin, wanda kawu ne ga yaron, ya kashe shi ta hanyar like masa baki da salatif sannan ya ci gaba da neman kudin fansar, inda ya amince zai karbi Naira miliyan biyu.

Kuma a lokacin da yake kokarin karbar kudin ne jami’an tsaro suka kama shi.

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Usman Na’abba Na’abba ya gamsu cewa shaidun da aka gabatar sun tabbatar da laifin da ake zarginsa, inda kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekara 14 a kan laifin yin garkuwa da mutane, laifin da ya saba da Sashe na 274 na Dokokin Final Kod.

Kuma kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan laifin kashe yaron da ya yi, a karkashin Sashe na 221 na Kundin Final Kod.

Barista A’isha Hassan Abdulkadir ce lauyar wanda ake tuhuma kuma ta bayyana rashin gamsuwarta da hukuncin, inda ta ce za su yi shawarar mataki na gaba da za su dauka.

Lauyan Gwamnati kuma mai gabatar da kara Barista Lamido, ya ce hukuncin ya yi musu daidai, lura da girman laifuffukan da ya aikata.

“Wannan hukunci ya yi daidai, domin an samu wanda ake zargin da hannu dumudumu wajen aikata laifuffukan.

“Mun gabatar wa kotun shaidu uku tare da shaidun manuniya hudu, ciki har da hoton yaron da aka kashe,” inji lauyan.

Aminiya ta ruwaito cewa, a watan Agustan bara ne wata Babbar Kotu a Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai shekara 35 hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kisan gilla.

Kotun dai ta yanke wa Nura Gwanda hukuncin saboda laifin da aka same shi da shi na daba wa wani dan shekara 27 mai suna Mudan Ibrahim wuka, wanda a dalilin haka ajali ya yi kiransa.