✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutumin da ya yi zanen batanci ga Annabi ya kone kurmus a hatsarin mota

Rahotanni sun ce duka su ukun sun kone kurmus, sai tokarsu aka tattara.

Mutumin nan dan kasar Sweden da ya yi zanen batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W.) a shekarar 2017, Lars Vilks, ya kone kurmus a wani hatsarin mota da shi da ’yan sanda biyu masu gadinsa.

Mai kimanin shekara 75, Lars dai ya sha fuskantar barazanar kashe shi bayan ya yi zanen batancin, inda har kungiyar Al-Qaida ta sanya la’adar Dala 100,000 ga duk wanda ya kawo shi.

Motar dai ta ci karo ne da wata ‘A-kori-kura’ sannan ta kama da wuta ranar Lahadi.

Rahotanni sun ce duka su ukun sun kone kurmus, sai tokarsu aka tattara, yayin da shi kuma direban motar A-kori-kurar aka garzaya da shi asibiti.

’Yan sandan kasar ta Sweden sun tabbatar da faruwar hatsarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP.

“Za mu bincika musabbabin hatsarin kamar yadda muke binciken kowanne irin hatsari. Saboda lamarin ya shafi jami’an ’yan sanda, an mika wa wani kwamitin bincike na ’yan sanda don fadada bincike,” injin kakakin ’yan sanda.

Sai dai ya ce babu wanda ake zargi da hannu a cikin harin.

Hatsarin dai ya faru ne a kusa da wani karamin gari mai suna Markyard, lokacin da motar ta Lars ta yi taho-mu-gama da A-kori-kurar da take tahowa, kuma dukkansu sun kama da wuta.

“Mutumin da muke karewa da wasu jami’anmu su biyu sun mutu a wani hatsari mai cike da takaici,” inji jami’in shiyya na ’yan sanda.